Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh.
Ma-abotan wannan shafi namu mai Albarka barkanmu da kasancewa daku a wannan lokaci.
To kamar yadda wannan shafin yasaba kawo muku abubuwan karuwa dan haka yauma yana tafe da shiri ma musaman domin wannan sanar muhimmiyar sanarwa ce daga kamfanin na (MTN) wanda yadace duk mai amfani da layin (MTN) ya kamata ya sani.
Sannan kamar dai yadda gwamnatin Nigeria ta sanar da hukumar sadarwa dasu kukkulle duk Domin a halin yanzu layukan daba'ai linking na NIN number ba, yakasan ce ana ta kulle wa mutane sama da mutane miliyan saba'in da biyu 72Millions.
Kamar yadda aka sanarwa kowane kamfanin layi dasu rufe layukan mutane wadanda ba'ai linking dinsu da NIN-Number ba kuma suka rufe din, to hakan ya sanya wasu miyagun mutane suka fito da wani sabon salo domin su cuci mutane ta hanyar fitar da link wanda suke yadashi a kafafen sada zumunta na sadarwa wanda suke yadashi da cewa ka shiga link din domin ka hade layinka da NIN-Numbar ka, kokuma ka bude layinka idan An rufe maka shi dalilin hakan ne yasa kamfanin MTN ya fitar da wata sanarwa ta,
Kamfanin MTN din sun fitar da sanarwar gargadin cewa: suna gargadin mutane akan wannan link din da ake turawa mutane subi domin su hada numbar su da NIN-Number, domin haka Muddin yakasance kun hadu da irin wannan links karka shiga ko ka latsashi domin ba daga su bane, su basu fitar da wani links da zakabi ka hada layinka da NIN-Numbar kaba don haka kar mutum yayi gaggawar kuskura yabi irin wannan links din da zarar ya ganshi, saboda links ne na 'yan damfara masu satar bayanan mutane don haka sai a kiyaye.
HANYOYI 5 BIYAR DA ZA KUBI WAJEN HADA LAYIN KU DA NIN NUMBER NA MTN SUNE KAMAR HAKA
> Zaka danna *785# sai NIN-Number
> Zaka iya tura sako ta hanyar rubuta NIN da manyan Baki, saika tura zuwa wannan number [785]
Misali kamar haka: NIN 60835671490
Sai ku danna kalmar Send to wannan number [ 785] shikenan.
>Sannan zaka iya magana da wakilansu koka kirasu ko kuma kayi magana dasu ta whatsapp da wannan numbar:- +234903300001.
>Sannan zaka iya kuma ka ziyarci website dinsu kamar haka: www.mtn.Ng
>Hanya ta 5 biyar zaka iya kuma ka dauko Application dinsu Mai suna My MTN App ka hada NIN-Numbar ka da layinka ta ciki wanda itama hanyace ingan tacciya.
Wadannan sune hanyoyi guda biyar da zaku iya hade linkimg na [MTN] da NIN number ku, sabanin wadannan hanyoyi guda biyar da suka bayar.
Na Gode Da Lokacin Da Kuka Bayar Domin Karanta Jawabina. Kuna Iya Barin Sharhi/Comment A Cikin Sashin Akwatin Sharhin Da Ke Kasa. Kada ku manta kuyi sharing kuma kuna iya ku biyo ni don ƙarin labarai Na Ilimantarwa.
Comments