Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh.
AMFANIN TUFFA (APPLE);
AMFANIN TUFA:-Shan Tuffa daya a rana na kawar da cututtuka da dama, kuma yawan shansa na rage tsufa da wuri.musamman Idan ana son maganin rage tsufa, Sai a rika sayen Tuffa ana sha. Yin hakan na rage bayyanar tsufa a jiki da fuska, Tuffa na dauke da sinadaran (Bitamin C / A).
Yadda Zaku Yi Amfani Da Tuffa Domin Rage Tsufar Fuska Ko Fata.
Bawon Tuffa:
Bawon Tufa na dauke da sinadaran gyaran jiki da kuma kare fata daga kodewar rana yayin da aka shige ta, don haka yana da kyau a rika shan wannan dan itace domin samun lafiyar fatar jiki.
Ayaba Da Tuffa:
Ayaba da Tuffa:-Ayaba na dauke da sinadarin gyaran fata tana tauke da (Bitamin A/ B/C, Yin amfani da ita a fata mai gautsi na gyara fata.
A kwaba ayaba bayan an bare ta sai a hada ta da markadadden Tuffa a kwaba da dama kafin a shafa a fuska. Za a iya zuba zuma ko nono/kindirmo kadan a wannan hadi.
A shafa a fuska na tsawon minti talatin 30 sai yayi kafin a wanke.
Lemun Tsami Da Tuffa:
Asamu Lemun tsami da Tuffa da kindirmo/nono:- Wannan hadin na sanya sulbin fuska a markada Tuffa sannan a matsa ruwan lemun tsami da kindirmo/nono, sai a kwaba. A shafa a fuska Sai a wanke bayan minti ashirin20 ko talatin30 .Wannan hadin na sanya laushi da sulbin fata da kuma daɗawa fata haske.
Tuffa Da Zuma:
Asamu Tuffa da zuma: A markada Tuffa sannan a zuba zuma cokali biyu a kwaba da kyau. Sai an wanke fuska da sabulu kafin a shafa kwabin da aka yi, Sai a wanke bayan minti talatin 30, Yawan amfani da wannan hadin, na sanya hasken fata.
Na Gode Da Lokacin Da Kuka Bayar Domin Karanta Jawabina. Kuna Iya Barin Sharhi/Comment A Cikin Sashin Akwatin Sharhin Da Ke Kasa. Kada ku manta kuyi sharing kuma kuna iya ku biyo ni don ƙarin labarai Na Ilimantarwa.
Comments