Assalamu alaikum
Kamar yadda wanan shafi ya shahara, wajan wayar da game da abubuwan da suka shafi fasahar yanar gizo, Yau muna tafe da darasi mai muhimman ci Zai yi kyau in duk wanda ya fara karanta farkon to ya samu ya kai karshe darasin🙏
Darasin Mu na yau zai yi magana ne akan wasu Applications na wayar Android phone Masu Matuƙar matsala ga duk wanda ya ke tarayya da su acikin wayar shi ta Android dan haka batare da dogon bayani ba ga Applications ɗin kamar haka.
1.Uc Browser
2.Clean Master
3.Es File Explore
4.Anti Virus App
5. Du.Battery Saver
Application a wayar Android suna da matuƙar amfani domin zaka samu dukkan wani shige da fice da masu riƙe da ita suke yi domin akwai Apps acikin ne don haka duk da app ɗin sun kasu gida-gida misali wani game, social media app, Banks app, Browser app, dukan su nau'i ne na Applications da muke mu'amullah da su a wayar Android sai dai wasu da ga cikin app ɗin basu da amfani in kai ku cutarwa ne ma ga ita wayar da me ita domin haka yana da kyau kafin ka sauke wani nau'in manhaja a wayar ka to kafara tabbátar da ingancin ta domin kaucewa shiga hatsari
Application na farko yana Ana Tuhumar shi da kasuwancin sai da bayanan wa'inda su ke amfani da shi kamar bayan Gmail don haka hatsari ne dukkan mai amfani da shi sai a kula.
Application na biyu wanna Applications yana da amfani mutuƙa sai dai fa yanzu yawanci sabbin wayoyin da suke shigowa suna ɗauke da wanan amfani da ya ke yi matsalar sa shi ne duk mai amfani da shi bayan ya kunna data zaiga Tallace tallace suna ya wo a saman wayar shi saidai shan data kawai domin haka ga wata hanya mai sauƙi domin share " Junk" na wayar Android, kai saye ku shiga setting na wayar ku sai ku danna App/Applications>storage>Clear Cache✓
Application na Uku kusan shima yana ɗauke da matsalolin sai dai shi ma kusan sabbin wayoyin yanzu suna zuwa da irin amfani da yake da shi a wayar sai dai manyan illolinsa suna da yawa ga su kamar haka.
Yana siyar da bayanan mutane batare da sun sani ba
Yana ɗauke da tallace tallace Da Masu yawa
Idan kun matsa lallai sai kun yi amfani da file 🗃️ a wayar ku to kuyi amfani da app mai inganci kamar "FILE GO" mallakar kamfanin Google yana da ingancin sosai.
Application na 4. Amity Virus application suna da yawa sai da babbar matsalar kusan dukkan su sukan tambayi permissions ga duk wanda ya son yay amfani da shi irin su; Location,Call, message,file, da dai sauran su sai dai sukan tura da bayanan ga wasu kamfani da ban batare da Neman izinin mai ɗauke da bayanan ba don haka sai a kula domin kusan yanzu wayoyin yanzu suna zuwa da amfanin wannan manhaja in kuma wayar ka bata duke da shi kuna iya garzaya wa play store domin suke wannan App domin a tabbatar da ingancin sa sosai "Play Protect Function.
Application na 5. Application ne kuma da ɗaɗɗe sai dai rashin amfanin shi ya fi amfani yawa masu ƙirƙirar wannan App sun ƙirƙire shine domin ya sanya waya ta cika da wuri cikin ƙanƙanin lokaci wato "fast change" da kuma sanya waya yin sauri yayin gudanar da aiki cikin sauri Sia dai duk wannan kamar yaudara ce domin ba wani app mai ƙarama waya saurin chagi sai dai ma ya sanye domin shi wannan App koda yaushe a kunne ake da buƙatar a barshi a kan waya, ga kuma tallace tallace da mai amfani da wayar kila baya so, domin kaucewa irairan irin waɗannan App sai kun yi taka tsan-tsan Fatan Allah ya bamu Sa'a Amiin. ****
Comments