Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh.
Kamar yadda wannan shafi yasaba kawo muku abubuwa na ilimantarwa yau ma yana tafe da shiri mai matuƙar amfani kamar yadda zaku karan a kasa asha karatu lafiya.
AMFANIN DABINO:
Dabino yanada matukar amfani a jikin dan Adam, domin Manzon Allah (S.A.W) ya kasance mai son Dabino, har ma yace "Idan kunyi azumi, to Dabino ya zama abunda
zaku fara ci (buda baki) dashi, idan babu dabino, to ku samu wani ɗan ɗan itace kamar kankana ko tufa.
> Yana saurin narkarda
abinci.
> Yana Sanya kuzari yayin Ibadar Aure.
> Yana taimakawa wajen kara jini.
> Yana taimakawa Ma'aurata maza/mata.
> Yana Maganin Basir Mai sa tsugunni a bayi.
> Yana karawa Ido lafiya
> Yana Rage Nauyin kiba/ teba.
> Yana Maganin Gudawa
> Yana Saurin Saukarda Hawan jini.
> Yana taimakawa kwakwalwa wajen Samun basira.
> Yana kariya daga Sihiri.
> Yana taimakawa Mata masu ciki dan samun sauqi wajen haihuwa.
> Yana kariya daga Sihiri.
YADDA ZA'AYI AMFANI DA DABINO WAJAN MAGANCE CIWON NONO GA MACEN DA TA HAIHU KO TAKE SHAYARWA
Asamu dabino guda bakwai7sai a ci sannan asha man tafarnuwa
karamin cokali sau ɗaya1 arana kwana uku.
DOMIN SAMUN NI'IMA GA MA'AURATA:
Ana daka dabino a zuba cikin madara (milk) sannan a saka Zuma a ciki a sha awa daya kafin a kwanta.
GA MATA MASU JUNA BIYU:
Ana cin dabino kwara bakwai7 kullum da safe idan lokacin haihuwa ya gabato Wannan yana hanawa macce yawan zubar jini lokacin haihuwa da iznin Allah.
MASU GUDAWA:
Ana daka garin dabino a saka a ruwan zafi a sha In shaa Allahu yana tsayar da gudawa.
INGANTA LAFIYAYYAR FATA:
Ana hada garin dabino da zuma da man zaitun a shafa a fuska tsawan awa daya
sai a wanke fuskar da ruwan ɗumi wannan yana saurin gyara fuska.Dadin daɗawa bin cike ya nuna Yawaita cin dabino na hana kamuwa da ciwon "CANCER" Haka Kuma MANZON ALLAH (S A W)
YACE DABINO AJWA YANA MAGANIN DUKKAN CUTATTUKA, KUMA DUK RANAR DA KACISHI,BABU WATA CUTA DA ZATA SAMEKA A WANNAN RANA, KO KUMA SAMMU KO SIHIRI.
Wasu Daga cikin maluman musulunci kuma sunce Annabi (S A W) Yana nufin kowanne dabino ba wai sai Ajwa ba (Allah ne masani).
YA ALLAH KA KARA MANA LAFIYA A JIKIN MU WAYANDA BASUDA LAFIYA KUMA ALLAH YA BASU LAFIYA.
Kuna Iya Rarraba Wannan Post Zuwaga 'Yan'uwa Da Abokan Arziki Kuma Ku Rubuta Sharhin Ku A Akwatin Ƙasa Hakan Zai Kara Karfin Gwiwa Domin Kara Ilimantar Daku.
Comments