AMFANIN SHAN KANWA GUDA GOMA
KANWA:
Kanwa ta kasance daya daga cikin ma'adinnan da ake samu a cikin wasu gurabe a kasashen Africa wacce ta kasance ita ba bishiya ba,ba wani ganye ko wata ciyawa ba,amma kuma wata hikima ta ubangiji tana da wani alfano/Amfani na daban dake zama waraka ga ajijkin ɗan Adam.
Kamar yadda aka sani kasar hausa akoi kanwa kala biyu,akoi wacce ake kira jar kanwa,tana da karfi sosai,akoi kuma wacce ake kira kanwar tuwo wacce ba-ja tana da ban-banci,bata da karfi sosai.
Duba da binciken da masana sukayi kanwa tana da mutukar amfani sai dai kuma hardama rashin amfani ga bayanin a takaice:
>:-kanwa na kontarda kornafi ko tashin zuciya.Idan dattin ciki yaiyi yawa a cikin mutum yakan iya haifar da tashin zuciya.Idan hakan ya faru to sai a nemi kanwa a jika a sha.inshaAllahu za a sami waraka.
>:-Sannan idan yaro karami wanda baya iya magana,ko *jinjiri na ta faman kuka aka rasa gane abinda ke damunsa to a nemi jar kanwa a gasa a wuta sai a jefa a cikin ruwa a karamin cup idan ta jika (medium solution) sai a karanta fatiha kafa goma a tofa a bashi ya sha.InshaAllahu za a dace.
>:-kumburin ciki : Idan aka ci abinci amma sai cikin ya kumbura to sai a nemi kanwa da ruwa mai kyau a jika a sha sau biyu a cikin sa'oi uku.
>:-Saurin narkarda abinci: Wasu sukan dauki lokaci mai tsawo suna fama bayan da suka ci abinci wanda baya saurin narkewa sai a dauki lokaci mai tsawo ciki a takure.Matsala irin wannan sai a nemi kanwa a jiqa a sha.
>:-kanwa na rage tsamin abinci.Idan abinci yaiyi tsami kamar miyar ganye/ tumatir ko wani ganye haka to sai a jefa kanwa kadan zata daidaita tsamin ya zamo daidai da yanda ake bukata.
>:-Ciwon ciki : A wasu lokutan haka kawai zaka ji cikin naka na murdawa ko yana ciwo ka rasa sanin dalili.Anan za ka iya neman kanwa ka jika ka sha musamman.ga yara kanana wanda basu iya magaba.
>:-Taurin bayan gari da yawan sakin iska sanadin wata matsala.Sai a nemi kanwa a jika da ruwan dumi a dinga sha a hankali.
SAI DAI KUMA DUDA WANNAN AMFANIN TANA ƊAUKE DA ILLOLI SUNKASU KAMAR HAKA:
Yawaita shan kanwa na ragewa namiji yawan maniyi.Wannan bincikene kuma ya tabbata.A dan haka,shawara ga maza da suguji amfani da kanwa ba tare da uzuri babbaba.kuma a san yanda za a sha.
A wani bincike da wasu masana harkar magani da hadin guiwar biochemistry department dake a Bells University a Ota ya nuna cewa shan kanwa na illata matse matsin namiji ta yanda zai iya shafuwar da kwayoyin haihuwar namiji.
Sun kara da cewa a sanadin yawan sodium dake tare da kanwa yawan shanta na iya janyo rauni ko wani lahani ga koda da kuma hanta.
sai dai kuma idan dai aka kiyaye da yanda ya dace a sha kanwa,to ba wani illa da zata haifar.
Kuna Iya Rarraba Wannan Post Zuwaga 'Yan'uwa Da Abokan Arziki Kuma Ku Rubuta Sharhin Ku A Akwatin Ƙasa Hakan Zai Kara Karfin Gwiwa Domin Kara Ilimantar Daku.
Comments