AMFANIN MANKADANYA GA DAN ADAM
Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh.
Man kadanya na da matukar amfani a fata domin yana dauke da sinadarai da dama har da sinadarin bitamin A /E.
Wannan man na magance kurajen fuska da gautsin fata da kodewar fuska da kuma kyasbi. Amfani da wannan man na sanya sulbin fata. Ga kadan daga cikin amfanin man kadanya.
>:- Domin Magance Kurajen Da Suke Futowa Idan Anyi Aski Ga Maza:
A samu man "Rosemary" da man kwakwa sannan a zuba a kan man kadanya a kwaba.
A rika shafawa a kulum bayan an aske gemu. Yana warkar da kurajen da ke fesowa a gemu bayan an yi aski.
>:- Magance Makero/Maƙenkero:
A samu man kadanya a hada shi da man zaitun sannan a rika shafawa a inda makeron yake a kullum da ikon Allah za-asamu sauki.
>:-Gamasu San Sulbin Fata:
Sai su yawaita shafa man kadanya a jiki bayan an yi wanka na sanya sulbin fata sannan yana hana fesowar wadansu cuttukan fata.
>:- Kitso:
Kitso da man kadanya na magance fatar kai daga makero sannan yana sanya gashi laushi da tsayi da kuma sulbi.
>:-Hadin Magance Kyasbi:
A samu man sandal da man ‘labender’ a zuba a cikin man kadanya sannan a kwaba sosai sannan a samu murta a zuba hadin.
A mayar da wannan man ya zama tamkar man shafawa a kullum.
A yi amfani da shi na tsawon watanni shida za a ga canji A samu man kwakwa da man zaitun da kuma man ‘almond’ sannan sai a zuba a murta a zuba man kadanyan a ciki sannan sai a kwaba da cokali ya kwabu sosai sannan sai a rika shafawa a jiki a mayar da man, man shafawa bayan an yi wanka.
>:-Domin Magance Bushewar Laɓɓa:
A samu zuma da man zaitun sannan sai a zuba a kan man kadanya a kwaba sosai. Sannan a sa a wuri mai sanyi . Sai a rika shafawa a labban baki a kullum za a samu sauki.
Kuna Iya Rarraba Wannan Post Zuwaga 'Yan'uwa Da Abokan Arziki Kuma Ku Rubuta Sharhin Ku A Akwatin Ƙasa Hakan Zai Kara Karfin Gwiwa Domin Kara Ilimantar Daku.
Comments