AMFANIN SHAN RUWAN GA LAFIYAR DAN ADAM
Dayawa musamman mata ba su damu da yin amfani da ruwan dumi ba, to lallai daga yau ki sani cewa ruwan dumi na da matukar mahimmanci ga jikinki.
Ruwan dumi yana kara wa mace lafiya a jikinta fiye da jikin namiji. Idan dai baki yin amfani da ruwan dumi a jikinki, to daga yau yana da kyau ki fara za ki sha mamakin yadda jikinki zai koma.
1> Ruwan dumi:- yana taimaka wa mace wajen kashe mata wasu kwayoyin cuta idan tana tsarki da shi. Yana kuma kara mata ni’ima a matsayinta na matar aure.
2> Idan mutum yana shan ruwan sanyi yana kara wa na’urar jiki lafiya. Yana kara wa jikin karfi da walwala ta yadda kowani bangare yayi aiki yadda ya kamata.
3>Shan ruwan dumi:> yana kara karfin makwogoro, ta yadda muryar mutum zai fita kamar wajen karatu ko kuma wajen bayani ta yanda mutane za su fahimta
4> Ruwan dumi:- yana kara dankon zamantakewar aure, idan mace tana yin tsarki da ruwan dumi yana kara mata ni’ima ta yadda mijinta zai gamsu da ita.
5> Ruwan dumi:- yana zama kariya ga mace wurin kamuwa da cututtuka idan tana yin wanka da shi. yana kuma gyara wa mace fata ta yi kyalli ba tare da kin yi bilicin ba.
6> Ruwan dumi:- yana mikar da hanjin ciki lokacin da suka tattari sakamakon yunwa ko kuma an yi azumi. Ina bukatar idan mutum ya dade bai ci abinci ba, to idan ya zo zai ci ya fara da abu mai zafi domin ya mikar da hanjinsa kafin wani abincin da bai da zafi.
Na Gode Da Lokacin Da Kuka Bayar Domin Karanta Jawabina. Kuna Iya Barin Sharhi/Comment A Cikin Sashin Akwatin Sharhin Da Ke Kasa. Kada ku manta kuyi sharing kuma kuna iya ku biyo ni don ƙarin labarai Na Ilimantarwa.
Comments