Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh.
SHIN MUNSAN MUHIMMANCIN AMFANI DA GANYAN SHUWAKA KUWA?
GANYAN SHUWAKA :
Ganye ne mai mutuƙar ɗaci mai kuma matuƙar magani ga lafiyar jikin ɗan adam wadda akan iya kiranta da turanci (Bitter Leaf) sai kuma sunanta na kimiya wato (vernonia amygdalina) shuwaka tana tsirowa a mafi yawan ɓangarorin Afirka, sannan ana amfani sosai da ita a gargajiyan ce.
Sannan a tarihance, ana amfani da ganyen a matsayin magani don cutuka da yawa daga zazzaɓin cizon sauro, taifod,ciwon sukari,gudawa tarin fuka,gallstone da cutar koda, zuwa rigakafin cutar kansa da rage hauhawar jini.
Tana kuma ɗauke Da Sinadarin Da Zasu Iya Taimakawa Mai Cutar Sikari:
Shuwaka na iya taimakawa mai ciwon sukari Binciken da aka buga a cikin Jaridar Kimiyyar Halittu ya nuna cewa kasancewar kwayoyin halitta, bitamin da sauran abubuwan gina jiki kamar sunadarai, lipids, carbohydrates, da sauran abubuwan da ake hadawa ana tunanin za su yi aiki tare don rage ƙarfin sukarin dake jiki mutum.
Tambaya:
Shin Ganyen Shuwaka Na Taimakawa Wajen Magance Rashin yin Bacci/dawuri?
Amsa:
"Eh"
Wasu sukan kan kasa yin bacci da daddare sakamakon wani damuwa ko tunanin wani abu daban to shan ruwan shuwaka da daddare, kafin kwanciyar bacci zai kawo nutsuwa da annashuwa wanda yake taimakawa wajen samuwar Isheshen bacci.
Shin Ganyen Shuwaka Na Samar Da Ƙwayoyin Haihuwa?
Shuwaka na iya samar da sakamako mai kyau kan ingancin maniyyi. Gabaɗaya, yawan sinadaran dake cikin Shuwaka suna da amfani ga lafiyar gaban namiji, don haka zai zama da amfani ga ma’aurata masu ƙoƙarin ɗaukar juna biyu yin amfani da ita a ko da yaushe.
Shuwaka Tana Taimakawa Wajen Magance Yawon Zazzaɓi:
Shuwaka tana ɗauke da (flavonoids) wanda ke da tasirin (Antioxidant) kuma suna taimakawa tare da magance matsaloli daban-daban na lafiya kamar zazzabi mai zafi Musamman ana amfani da ganyen shuwaka a tarihin gargajiya don maganin ƙwayoyin cuta na zazzaɓin taifot da zazzaɓin cizon sauro.
Shin Shuwaka tana Da Sunadarai Da Zasu Iya Taimakawa Masu Hawan Jini?
Shuwaka na da kyau ga ƙashi da haƙora
Vitamin C babban ma’adanai ne na antioxidant da ake samu a cikin shuwaka wanda ke taka muhimmiyar rawa a cikin jiki, gami da kula da ƙasusuwa da haƙori.
Hakanan yana dauke da sinadarin "Bitamin K" wanda yake taimakawa jiki kula da lafiyar kasusuwa kuma tana hana raunin kashi, wanda aka fi sani da (osteoporosis).
Ganyen Shuwaka Yana Taimakawa Magance Ciwon Ciki:-Shuwaka magani ne na gargajiya don ciwon ciki. Wani bincike a cikin mujallar (Toxicology Reports) ya nuna cewa tsiron na iya bada kariya daga cutar Olsa. Binciken ya nuna cewa (Antioxidants) dake cikin shuwaka suna ba da gudummawa ga tasirin waɗannan cuttuka.
Shuwaka Yana Taimakawa Wajen Yakar Cutuka Marasa Tsari:
Wani sinadarai a cikin shuwaka shine bitamin E, wanda ke aiki a zaman antioxidant tana yaƙi da ƙwayoyin cuta waɗanda ke da lahani jikin dan adam.
Abin Lura:
Yadda ya kamata kayi amfani da ganyen Shuwaka a gargajiyan ce shine, zaka iya amfani da Shuwaka ta hanyar tauna ɗanyun ganyen ka haɗiye ruwan. Ko kuma, zaku iya daka danyen ganyen a cikin turmi kuma a fitar da ruwan Zaku iya sa ɗan gishiri a ciki don zai sirka ta.
Kuna Iya Rarraba Wannan Post Zuwaga 'Yan'uwa Da Abokan Arziki Kuma Ku Rubuta Sharhin Ku A Akwatin Ƙasa Hakan Zai Kara Karfin Gwiwa Domin Kara Ilimantar Daku A fasahance.
Comments