Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh.
Wannan wata hanya ce da zata baka damar kashe kiran da zai shigo layinka amma kuma zaka yi kira kuma zaka yi chat domin wani lokaci kanaso kayi amfani da wayarka, kamar kanaso kayi chat ko kuma amfani da internet kawai batarwbda wani ya kira kaba don zai iya katse ma ka abinda kake yi da wayarka kuma bakaso a dameka da kira, sannan wani lokacinma idan ka fara wani abu aka kiraka zai iya dawo dakai baya sabida kiran.
Sanan wannan hanya tanada matukar amfani sosai don zaka samu damar amfani da network din wayarka ba tare da fargabar wani zai iya kirankaba.
Sannan wannan hanya ba sai kana amfani da android ba ko keypad duk zaka iya amfani da ita saboda bada wani application bane zamuyi amfani ko wata platform.
Da farko zaku shiga dialler na wayarku sai ka danna wannan number kamar haka * * 21 * saika hada number guda goma shadaya ka danna # a ƙarshe sai ka danna wajan kira kamar haka (* * 21 * 0123456789#) sanna kuma ko wace irin number ka haɗɗa ba zatayi ba matsala abun buƙata shine kawai ka saka numbers din, bayan ka kira zakaga ya nunamaka rubutu maka alamar forward wato yanzu wmlayin ka yana forward zuwa wadancan numbers din da ka saka, idan kayi haka duk wanda ya kiraka za'a cemasa ba dai dai ya saka number takaba har sai ka cire daga forward din.
To bayan kuma ka gama.
Yadda Ake Cirewa;
Yanda zaka cire bayan ka gama abinda kakeyi sai ka koma cikin dialler ka danna #21# sai ka kira zakaga sun nunama deacctive wato ka cire numban taka daga hana kowa kiranka, daga nan layinka ya koma yanda yake yan zu kowa yana da damar kiran ka.
Idan Kuma Kuna Da Wasu Karin Wani Labari/Jawabi Da Kuke Ganin Yakamata A Saka A Cikin Wannan Website Wanda Zai Iya Taimaka Wa Wasu Ko Kuma Idan Akwai Wani Gyara Da Ake Buƙata Inyi, Don Allah Ku Tabbata Kun Faɗakar Da Ni Ta Amfani Da Sashin sharhi/Comment Na Kasa Ko Ta haryar Tuntuba Na Hanyar Sadarwa Ina Matukar Godiya Da Farin Cikin Yayin Da Kuka Bada Lokacin Ku Kuka Ziyarci Shafina Don Karanta Wa Daga Cikin Abubuwan Dana Wallafa Nagode 'Yan'uwana.
Comments