**
Assallamu Alaikum
Bayani Dalla -Dalla Game Da Kudin Cizo Da Yadda Ake Maganceshi
Kuɗin cizo wani ƙaramin kworo ne ,da yake iya addabar rayuwar ɗan adam yayin da yake tsaka da bacci domin shi kudin cizo yafi samun damar wall-wala da dare domin duhun dake cikin sa baya iya samun damar rayuwa cikin haske.
Kuɗin cizo wanda a turance ake kira da bed-bug an raba sunnan shi ne saboda addabar ɗan adam da yake yi misali kamar butterfly ba shi ba a rabawa misali butter-fly 🦋 domin shi baya addabar ɗan adam.
Shin ko Kuɗin cizo yana haddasa kwayoyin cuta?
Maganar gaskiya shine ba'a tan-tance wata cuta ba wacce ake alaƙan tata da wannan kworo ba sai dai a wasu ƙasashe irin su America ana alaƙanta su da suna iya yaɗa kwoyoyin cuta ta Trypanosoma masu sa ciwon sammore sai dai mu annan kasar tamu kworon da yake iya yaɗa wanan cuta shi ne kudan tsando kamar yadda shafin aminta ya ruwaito.
Shin tayaya ake samun su ?
Wannan kworo yana da mutukar hatsari sosai musamman in ya samu muhallin da ba'a yawan kula dashi don haka in ya kasance muhalli ana yawan bashi kulawa to wanan kuɗin cizo baya iya zama.
Yadda ake kawar da kuɗin cizo a gida ko ɗaki;
Gaskiya akwai matukar wahala kawar da wannan kwaro daga gida ko a ɗaki domin shi wannan kworo yakan iya ɓuya a wajajan da ba'a tsammani don haka sai an kula matuƙa.
Hanyoyi biyu da za'a iya bi don kawar da Kuɗin cizon;
1. Da zarar hanfahimci akwai wanan kworo a cikin gida ko muhallin ku to kuyi gaggawar sayo Maganin kwori mai kyau ku feshe dakin gaba-daya dukkan wani sako ko lungu da rami duka yana da kyau a kula sosai wajan ganin an saka wannan maganin kuma abi matakan anfani da maganin kada kuma garin neman ido a rasa gira.
2. Kuna iya fito da dukkan wani kaya daga cikin ɗakin sannan ku wanke Sai dai kuma zaifi kyau ku wanke da ruwan zafi domin Kuɗin cizo baya san ruwan zafi kashe shi yake sosai ba sai kun sanya wa kayan ku wani nau'in maganin mai ɗauke da sinaidarai ba sai ku shanya su a rana su bushe.
Don kaucewa don kada su shiga muhallin ku;
Yanada kyau mudunga kula da wajajan da muke zama misali Mota ,guraren taron jama'a,otal
Domin duka wannan guraren ba'a rasa wannan kworo kai har cikin jakunkuna na wasu matan ko kaya sai a kula sosai in kunyi mu'amulla bayan kun rabu kuna karkaɗe tufafin ku.
**
Comments