Skip to main content

Posts

Showing posts from April, 2022

AMFANIN CIN DABINO GA LAFIYAR DAN ADAM

Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh.  Kamar yadda wannan shafi yasaba kawo muku abubuwa na iliman tarwa yau ma yana tafe da shiri mai matuƙar amfani kamar yadda zaku karan a kasa asha karatu lafiya.    AMFANIN DABINO: Dabino yanada matukar amfani a jikin dan Adam, domin Manzon Allah (S.A.W) ya kasance mai son Dabino, har ma yace "Idan kunyi azumi, to Dabino ya zama abunda zaku fara ci (buda baki) dashi, idan babu dabino, to ku samu wani ɗan ɗan itace kamar kankana ko tufa. > Yana saurin narkarda abinci. > Yana Sanya kuzari yayin Ibadar Aure. > Yana taimakawa wajen kara jini. > Yana taimakawa Ma'aurata maza/mata. > Yana Maganin Basir Mai sa tsugunni a bayi.  > Yana karawa Ido lafiya  >  Yana Rage Nauyin kiba/ teba.  > Yana Maganin Gudawa  >  Yana Saurin Saukarda Hawan jini. >  Yana taimakawa kwakwalwa wajen Samun basira. > Yana kariya daga Sihiri. >  Yana taimakawa Mat...

AMFANIN KANWA TARE DA ILLOLINTA

        AMFANIN SHAN KANWA GUDA GOMA      KANWA: Kanwa ta kasance daya daga cikin ma'adinnan da ake samu a cikin wasu gurabe a kasashen Africa wacce ta kasance ita ba bishiya ba,ba wani ganye ko wata ciyawa ba,amma kuma wata hikima ta ubangiji tana da wani alfano/Amfani na daban dake zama  waraka ga ajijkin ɗan Adam. Kamar yadda aka sani  kasar hausa akoi kanwa kala biyu,akoi wacce ake kira jar kanwa,tana da karfi sosai,akoi kuma wacce ake kira kanwar tuwo wacce ba-ja tana da ban-banci,bata da karfi sosai. Duba da binciken da masana sukayi kanwa tana da mutukar amfani sai dai kuma hardama rashin amfani g a bayanin a takaice: >:-kanwa na kontarda kornafi ko tashin zuciya.Idan dattin ciki yaiyi yawa a cikin mutum yakan iya haifar da tashin zuciya.Idan hakan ya faru to sai a nemi kanwa a jika a sha.inshaAllahu za a sami waraka. >:-Sannan idan yaro karami wanda baya iya magana,ko *jinjiri na ta faman kuka aka rasa g...

AMFANIN MAN KAƊANYA GA LAFIYAR MU

AMFANIN MANKADANYA GA DAN ADAM Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh. Man kadanya na da matukar amfani a fata domin yana dauke da sinadarai da dama har da sinadarin bitamin A /E.  Wannan man na magance kurajen fuska da gautsin fata da kodewar fuska da kuma kyasbi. Amfani da wannan man na sanya sulbin fata. Ga kadan daga cikin amfanin man kadanya. >:- Domin Magance Kurajen Da Suke Futowa Idan Anyi Aski Ga Maza: A samu man "Rosemary" da man kwakwa sannan a zuba a kan man kadanya a kwaba.  A rika shafawa a kulum bayan an aske gemu. Yana warkar da kurajen da ke fesowa a gemu bayan an yi aski. >:- Magance Makero/Maƙenkero: A samu man kadanya a hada shi da man zaitun sannan a rika shafawa a inda makeron yake a kullum da ikon Allah za-asamu sauki. >:-Gamasu San  Sulbin Fata: Sai su yawaita shafa man kadanya a jiki bayan an yi wanka na sanya sulbin fata sannan yana hana fesowar wadansu cuttukan fata. >:- Kitso: Kitso da man kadanya na magan...

AMFANIN ZOGALE DA YADDA AKE AMFANI DA SHI DON INGANTA LAFIYA

Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh. AMFANIN  ZOGALE A JIKIN ƊAN  ADAM  DA YADDA AKE AMFANI DA SHI >:-Ga mai fama da sanyin kashi ko wani kumburi zai soya 'ya'yan zogale a daka su sannan a hada da man kwakwa (man-ja) sai a shafa. >:- Ana dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin maganin olsa (ulcer). >:- Ga wanda ya yanke ko ya sare ko wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen ganyen zogale inshaAllah jinin zai tsaya. >:-Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin zogale da man zaitun ya shafa. >:-Ana sanya garin zogale akan wani rauni ko gembo domin saurin warkewa.   >:-Sanya garin zogale a cikin abinci yana maganin hawan-jini da kuma karama mutum kuzari. >:-Ana shafa danyen ganyen zogale akan goshi domin maganin ciwon kai. >:-Ana dafa ganyen zogale tare da sa kanwa 'yar kadan domin maganin ciwon shawara. >:-Ga mai fama da ciwon ido zai diga ruwan danyen zogale, haka ma mai fama da ciwon kunne. ...

AMFANIN GANYEN SHUWAKA

Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh. SHIN MUNSAN MUHIMMANCIN AMFANI DA GANYAN  SHUWAKA KUWA? GANYAN SHUWAKA : Ganye ne mai   mutuƙar ɗaci mai kuma matuƙar magani ga lafiyar jikin ɗan adam wadda akan iya kiranta da turanci (Bitter Leaf) sai kuma sunanta na kimiya wato (vernonia amygdalina) shuwaka tana tsirowa a mafi yawan ɓangarorin Afirka, sannan ana amfani sosai da ita a gargajiyan ce. Sannan a tarihance, ana amfani da ganyen a matsayin magani don cutuka da yawa daga zazzaɓin cizon sauro,  taifod, ciwon sukari, gudawa tarin fuka, gallstone da cutar koda, zuwa rigakafin cutar kansa da rage hauhawar jini. Tana kuma ɗauke Da Sinadarin Da Zasu Iya Taimakawa Mai Cutar Sikari: Shuwaka na iya taimakawa mai ciwon sukari Binciken da aka buga a cikin Jaridar Kimiyyar Halittu ya nuna cewa kasancewar kwayoyin halitta, bitamin da sauran abubuwan gina jiki kamar sunadarai, lipids, carbohydrates, da sauran abubuwan da ake hadawa ana tunanin za su yi aiki tare...

KARANTA AMFANIN TUFA(APPLE)

Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh. AMFANIN TUFFA (APPLE); AMFANIN TUFA:-Shan Tuffa daya a rana na kawar da cututtuka da dama, kuma yawan shansa na rage tsufa da wuri.musamman Idan ana son maganin rage tsufa, Sai a rika sayen Tuffa ana sha. Yin hakan na rage bayyanar tsufa a jiki da fuska, Tuffa na dauke da sinadaran (Bitamin C / A).  Yadda Zaku Yi Amfani Da Tuffa  Domin Rage Tsufar Fuska Ko Fata. Bawon Tuffa:  Bawon Tufa na dauke da sinadaran gyaran jiki da kuma kare fata daga kodewar rana yayin da aka shige ta, don haka yana da kyau a rika shan wannan dan itace domin samun lafiyar fatar jiki. Ayaba Da Tuffa: Ayaba da Tuffa:-Ayaba na dauke da sinadarin gyaran fata tana tauke da  (Bitamin A/ B/C, Yin amfani da ita a fata mai gautsi na gyara fata.  A kwaba ayaba bayan an bare ta sai a hada ta da markadadden Tuffa a kwaba da dama kafin a shafa a fuska. Za a iya zuba zuma ko nono/kindirmo kadan a wannan hadi.  A shafa a fuska na tsawon ...

KUNA IYA KASHE DUK WANI KIRA DA ZAI SHIGO WAYAR KU, TA WANNAN HANYAR

Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh. Wannan wata hanya ce da zata baka damar kashe kiran da zai shigo  layinka amma kuma zaka yi kira kuma zaka yi chat domin wani lokaci kanaso kayi amfani da wayarka, kamar kanaso kayi chat ko kuma amfani da internet kawai batarwbda wani ya kira kaba don zai iya katse ma ka abinda kake yi da  wayarka kuma bakaso a dameka da kira, sannan wani lokacinma idan ka fara wani abu aka kiraka zai iya dawo dakai baya sabida kiran.  Sanan wannan hanya tanada matukar amfani sosai don zaka  samu damar amfani da network din wayarka ba tare da fargabar wani zai iya kirankaba. Sannan wannan hanya ba sai kana amfani da android ba ko keypad duk  zaka iya amfani da ita saboda bada wani application bane zamuyi amfani ko wata platform. Da farko zaku shiga dialler na wayarku sai  ka danna  wannan number  kamar haka  * * 21 * saika hada number guda  goma shadaya ka danna #  a ƙarshe sai ka danna wajan...

MUHIMMIN SANARWA MAI AMFANI

Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh. Ma-abotan  wannan shafi namu mai Albarka barkanmu da kasancewa daku a wannan lokaci.  To kamar yadda wannan shafin yasaba kawo muku abubuwan karuwa dan haka yauma yana tafe da shiri ma musaman   domin wannan  sanar  muhimmiyar sanarwa ce daga kamfanin na  (MTN) wanda yadace duk mai amfani da layin (MTN) ya kamata ya sani. Sannan kamar dai yadda gwamnatin Nigeria ta sanar da hukumar sadarwa dasu kukkulle duk Domin a halin yanzu layukan daba'ai linking  na  NIN number ba, yakasan ce ana ta kulle wa   mutane sama da mutane miliyan saba'in da biyu 72Millions. Kamar yadda aka sanarwa kowane kamfanin layi dasu rufe layukan mutane wadanda ba'ai linking dinsu da NIN-Number ba kuma suka rufe din, to hakan ya sanya wasu miyagun  mutane suka fito da wani sabon salo domin su cuci  mutane ta hanyar fitar da link wanda suke yadashi a kafafen sada zumunta na sadarwa wanda ...

AMFANIN HULBA GUDA GOMA (10)

Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh. To kamar dai yadda akasaba wannan shafin ya kan kawo muku abubuwa na harkar ilimi yau muna tafeda shiri mai matukar amfani shiri ne da akan lafiyarmu dan haka taken wannan shiri shine . AMFANIN HULBA  GUDA GOMA GA LAFIYAR DAN ADAM 1>Ana iya maganin ulser da garin hulba, idan ake hada hulba cokali daya na hulba da cokali daya na zuma mara hadi mai kyau sai a-asha,  2>Hulba tana baiwa (Goolblader) Iganci, tana  Kara ingancin  sinadari  acikin jini, wanda hakan akarshe zata iya saukaka ciwan suga ga masu fama da ciwan suga, zaa yi wannan ta hanyar shan cokali daya na garin hulba mai kyau arana sau uku. 3>Hulba tana Kara  yawan ruwan no-no musamman ga mata masu shayarwa,shi yasa likitoci sukan bayar da shawara arika shan man hulba sau uku arana. 4>Hulba tana karama hanjin dan adam karfi tafuskar narkar da abinci, da kuma sauki wajen tafiyar sa. 4>Tana taimakawa maza wajen basu ni...

AMFANIN SHAN RUWAN ƊUMI GA LAFIYAR MU

Assalamu alikum warahmatullah wabarakatuh Dafatan duk muna lafiya. AMFANIN SHAN RUWAN GA LAFIYAR DAN ADAM Dayawa musamman mata ba su damu da yin amfani da ruwan dumi ba, to lallai daga yau ki sani cewa ruwan dumi na da matukar mahimmanci ga jikinki.  Ruwan dumi yana kara wa mace lafiya a jikinta fiye da jikin  namiji. Idan dai baki yin amfani da ruwan dumi a jikinki, to daga yau yana da kyau ki fara za ki sha mamakin yadda jikinki zai koma. 1> Ruwan dumi:- yana taimaka wa mace wajen kashe mata wasu kwayoyin cuta idan tana tsarki da shi. Yana kuma kara mata ni’ima a matsayinta na matar aure. 2> Idan mutum yana shan ruwan sanyi yana kara wa na’urar jiki lafiya. Yana kara wa jikin karfi da walwala ta yadda kowani bangare yayi aiki yadda ya kamata. 3>Shan ruwan dumi:> yana kara karfin makwogoro, ta yadda muryar mutum zai fita kamar wajen karatu ko kuma wajen bayani ta yanda mutane za su fahimta 4> Ruwan dumi:- yana kara dankon zamantake...